Mr Annan, wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya mutu ranar Asabar din da ta gabata a birnin Geneva, inda ya kwashe shekara da shekaru yana zaune da iyalinsa.
Mr Addo ya bayyana haka ne lokacin da wata tawagar mutum bakwai na iyalan tsohon babban jami'in diflomasiyyar ta ziyarce shi a gidan gwamnatin kasar da ke Accra.
Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu
Duniya na alhinin mutuwar Kofi Annan
A cewar sa, za a yi wa Mr Annan jana'izar ban-girma ranar 13 ga watan Satumba a matsayinsa na babban ma'aikacin diflomasiyya da kuma dan kasar na gari.
Ya kara da cewa gwamnatin Ghana ce za ta dauki nauyin dukkan abubuwan da za su faru lokacin jana'izar.
Shugaban kasar ta Ghana ya ce shugabannin kasashe da dama sun kira shi inda suka yi masa ta'aziyyar mutuar Mr Annan, yana mai cewa yana sa ran da dama daga cikin su za su halarci jana'izarsa.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment