Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi - arewastar arewastar: Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi

Pages

Featured Featured
how-to-use-your-android-device-as
Techwise Blogger Template By 24clan Team
dent-free-data
Liberty 3 Column Blogger Template By 24clan Team
9mobile-special-offer
Publisher V7.5.1 Premium - WordPress News Template By 24clan Team
mtn-double-data-cheat
Sahifa v5.6.10 Premium Wp Theme By 24clan


Friday, August 31, 2018

Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi

Rahotanni sun fallasa kasar Iran a matsayin kasar dake taimaka ma yan Shi’a da makamai don sun kaddamar da yaki a kasar Iraqi da sauran kasashen dake hamayya dasu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar arewainfinity. com.ng ta ruwaito kasar Iran na cigaba da karfafa mayakan yan shia dake kasar Iraqi mai suna Quds da makaman kare dangi watau nukiliya don su kare kansu tare da kai ma duk wata kasar dake yaki dasu hari.

Wani hadakar jami’an gwamnatin kasar Iran guda uku, jami’a leken asiri na kasar Iraqi da wasu jami’an kasashen turai ne ta bayyana haka, inda tace a yanzu haka Iran ta aika da makaman nukiliya masu kananan zango ga yan shi’ar kasar Iraqi a watannin da suka gabata.


Haka zalika wasu jami’an leken asiri guda biyar sun tabbatar da cewar Iran na taimaka ma yan shi’an Iraqi da kayan aiki domin su fara kera makamansu da kansu. “Hikimar yin haka shine don Iran ta samu tufun dafawa idan har an kai mata hari.

“Nukilyan da ta baiwa yan shi’an basu dayawa, basu wuce dozin daya ba, amma zasu iya kara yawansu idan bukatar haka ya taso.” Inji wani jami’in kasar Iran.

A baya kasar Iran ta sha yin ikirarin cewa makaman nukiliya da take kerawa zata yi amfani dasu ne kawai idan an tabata, amma sai ga shi da aka tambayi manyan jami’an kasar game da wannan batu sai suka zuke, suka ki cewa uffan.
Daga cikin makaman da yan shi’an kasar Iraqi suka samu akwai wasu nukiliyoyi masu suna Zelzal, Fateh-110, da Zolfaqar wanda zasu iya kai nisan kilomita 200 zuwa 700, wanda hakan ya sanya kasashen adawar Iran Isara’ila da Saudiyya cikin wannan zango.

Ku biyo mu

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar arewainfinity.com.ngHausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@arewainfinity.com.ng
Source: arewainfinity. com.ng



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment