Za a sake yi wa Saraki shari'a - arewastar arewastar: Za a sake yi wa Saraki shari'a

Pages

Featured Featured
how-to-use-your-android-device-as
Techwise Blogger Template By 24clan Team
dent-free-data
Liberty 3 Column Blogger Template By 24clan Team
9mobile-special-offer
Publisher V7.5.1 Premium - WordPress News Template By 24clan Team
mtn-double-data-cheat
Sahifa v5.6.10 Premium Wp Theme By 24clan


Tuesday, December 12, 2017

Za a sake yi wa Saraki shari'a

Kotun daukaka kara ta yankin Abuja ta tasa keyar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, zuwa kotun da'ar ma'aikata domin a sake masa sharia kan zargin rashin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa.
Gwamnatin Najeriya dai ta daukaka kara ne bayan kotun da'ar ma'aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan Najeriyar da farkon wannan shekarar.
Kotun da'ar ma'aikatar ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume 18 na rashin fadin gaskiya wajen bayyana kadarori da aka yi wa Saraki.
A zamanta a yau, kotun ta yanke hukuncin cewa Mista Saraki bai bayar da gamsasshiyar amsa kan uku daga cikin tuhume-tuhume 18 da aka masa ba.
Masu shari'ar uku da suka jagorancin zaman kotun karkashin alkali Tinuade Akomolafe-Wilson, sun yi watsi da sauran tuhume-tuhume 15 din da gwamantin Najeriyar ta yi wa Saraki.
Ana Tuhumar Bukola Saraki da rashin yin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa a lokacin da yake gwamnan jihar KwaraHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAna Tuhumar Bukola Saraki da rashin yin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara
Sai dai kuma wata sanarwa daga ofishin watsa labaran Bukola Saraki ta ce shugaban majalisar dattawan Najeriyar zai daukaka kara kan hukuncin.
Shi kuwa lauyan gwamnatin Najeriya kan shari'ar, Rotimi Jacobs, ya ce zai yi nazari kan hukuncin kotun kafin ya yanke shawara kan matakin da zai dauka.Kotun daukaka karar dai ta wanke Saraki a cikin shekarar 2017

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment